2019: Babu wata siyasa kan kudaden da muka ce dole Intels ta Atiku ta biya a sati biyu - inji Hadiza Bala tsohuwar Hadimar El-Rufai
- Zargin Atiku na handama ya gagara kaishi kurkuku
- Gwamnati ta taso kamfunnansa gaba, watakil tsoron karfinsa a 2019
- Hadiza Bala ta ce babu siyasa a aikinta
Kamani guda tilo da yafi tarawa Atiku Abubakar kudade, watau Intels Nigeria Limited, wanda ke Legas a tashar jiragen ruwa, wanda ke sauke mai da ayyukan hada-hadarsa shi-shi kadai shekaru kusan 20, ya shiga komar hukumar NPA.
An dai ce kamfanin ya biya miliyoyin daloli da ai ake binsa bashi kuma an yanka masa sati biyu ne kacal da ya biya su ko ya fuskanci fushin hukumar da takunkumai na aikace-aikace a gabar tekun ta Legas.
Tun bayan zuwanta hukumar Hadiza Bala, ta tsarkake ayyukan kamfanin da yawa, muamman kin biyan kudadena ga asusun gwamnati guda daya tilo, sannan ma da kin bayyana wasu abubuwa da gwamnati ta bukata, a zargin hukumar.
Kamfanin dai, shine kadai ke da ikon sauke mai a da, amma sabbin dokoki sun sanya dol aka rage masa karfi aka kawo wasu kamfunnan da zasu yi wannan aiki a gabar tekunn ta Legas.
A hirarta da TVC News, Abuja, Hadiza Bala Usman, tace lallai kam babu wata siyasa a cikin aikinta, domin sanya kowa take a hukumar yayi daidai.
DUBA WANNAN: Ana neman tsige shugaban majalisa Bukola Saraki
Sai dai, ganin cewa ita ta hannun damar El-Rufai ce, kuma ta hannun damar Buhari, wannan wasu na gan bi-ta-da kullin siyasa ake yi wa dan PDPn don kar ya sami kudin takara a 2019, musamman ganin sai yanzu ne aka sanya ma kamfanin ido.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng