Yan siyasa ke saya ma wasu makiyaya muggan makamai – Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kauta Hoore

Yan siyasa ke saya ma wasu makiyaya muggan makamai – Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kauta Hoore

Rikicin makiyaya da manoma dai ya ki ci, ya ki cinyewa a yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya. An yi asaran rayuka; na mutane da dabbobi a cikin sabuwar shekaran 2018 kadai.

A ranan 1 ga watan, an hallaka yan jihar Benue 70 ba gaira ba dalili, amma daga baya, wani jigo a kungiyar Miyetti Allah yace an kai harin ne saboda wasu sun sacewa Fulani shanayensu.

Su kuma yan kabilar Tiv tun lokacin suka fara da daukan fansa. Kwanaki biyu da suka gabata, an kona wasu makiyaya bakwai a jihar Benuwe ba gaira ba dalili.

Amma shugaban kungiyar Miyyeti Allah Kauta H, Alhaji Bello Abdullahi Badejo, ya bayyana cewa wasu yan siyasa ke sayawa makiyaya masu haddasa fitina makamai.

Yan siyasa ke saya ma wasu makiyaya muggan makamai – Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kauta
Yan siyasa ke saya ma wasu makiyaya muggan makamai – Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kauta

Ya bayyana hakan ne a wani hira da jaridar Sun inda yace:

"A makonni biyu da suka gabata, hukumar yan sanda ta damke wasu mutane da bindigaAK47 kuma bay an Fulani bane. Suna ambaton sunayen wasu yan siyasa cwa su suka saya masu makamai kuma na yarda da maganansu saboda talakan makiyayi bai zai iya sayan AK47 ba."

KU KARANTA: Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Zaku tuna cewa jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin shugaba Buhari ta ce zata baiwa kowani jiha daman dakile rikicin makiyaya da manoma yadda taga dama.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: