Dalilin da yasa dalibai basu sha'awar darasin lissafi
Hasashe na mafi akasarin masana ilimi ya tabbatar da cewa, ɗalibai da dama su kan gaza wajen sha'awar darasin lissafi musamman na makarantun sakandire, wanda har yanzu ake ta muhawarar gano ainihin inda fagen dagar yake domin tantance musabbabin wannan lamari.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne, wani malamin ilimi Mista Philip Balogun ya bayyana cewa, mafi akasarin ɗalibai su kan gaza wajen sha'awar darasin lissafi tare da rashin kwazo a sakamakon mawuyacin hali da malamai ke jefa ɗalibai a yayin karantarwa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Balogun wanda shine mataimakin shugaban makarantar Grace Group of Schools, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na Najeriya a jihar Legas.
Yake cewa, saboda wannan dalili ne ya sanya yara da dama tun suna ƙananan shekaru suke fara shayin lissafi a makarantun su.
KARANTA KUMA: Majalisar dokoki ta rattaba hannu a kan sabbin dokoki 9 a jihar Jigawa
Malamin ya ci gaba da cewa, akwai buƙatar malamai su ɗabbaƙar da nasibi wajen karantar da darasin lissafin domin sauƙaƙawa ɗalibai da sanya masu sha'awar sa a zukatansu.
Ya ƙara da cewa, akwai kuma buƙatar ɗalibai su lizinci nazarin kwamfuta domin samun wata sabuwar hanya ta tallafi da za ta faɗaɗa musu yalwar sauƙi wajen karatuttukan su na lissafi.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar dokoki ta jihar Jigawa, ta aminta da sabbin dokoki 9 cikin 15 da majalisar zartaswa da gindaya cikin kundin tsarin ƙasa a shekarar da ta gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng