Mutum 90 ake tsammani sun halaka a kifewar jirgin ruwa makare da 'yan gudun hijira
- Akwai yiwuwan 'yan hijira 90 sun rasa rayukan su yayin da jirgin da su ke ciki ta kifa a mahadan teku ta Libiya
- Baya ga wannan rashi, mutane 218 kenan su ka rasa rayukan su a wannan mahada a 2018
- Hukumar Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), ita ce ta bayyana hakan
Hukumar Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), ta bayyana cewar akalla mutane 90 ne su ka rasu a hatsarin da ya faru ga jirgin ruwan da ke dauke da su a teku ta bakin gaban Libiya.
Jirgin ruwan na su ta kife ne a ranar Juma'a a inda nan take ruwa ya koro gawawwaki 10 bakin tekun, 2 'yan Libiya, 8 'yan Pakistan. Wasu 2 kuma sun yi iyo sun tsira da ran su a yayin da kuma wasu masunta su ka tseratar da wani mutum 1.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya canja sunan Jami'a domin karama marigayi Alex Ekwueme
Hukumar ta sha gargadi a kan gujewa neman yin hijira zuwa turai ta tekun da ya hada Kasar Libiya da Italy. Baya ga wannan rashi, mutane 218 kenan su ka rasa rayukan su a kokarin yin hijira a wannan shekara ta 2018.
IOM ta bayyana cewar a mahadan teku na Kasashen Arewacin Afirika da Spain, mutane 28 sun rasa rayukan su. A mahadan teku kuwa na Turkiyya da Greece, babu wanda ya rasu a wannan shekara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng