Babagana Kingibe na nesanta kansa da sabbin fastocinsa da suka cika gari

Babagana Kingibe na nesanta kansa da sabbin fastocinsa da suka cika gari

- Fastocin Kingibe sun cika Abuja a makon nan

- Ya fito ya karyata sha'awarsa da kujerar

- A baya dai ya taba yin takara

Babagana Kingibe na nesanta kansa da sabbin fastocinsa da suka cika gari
Babagana Kingibe na nesanta kansa da sabbin fastocinsa da suka cika gari

Ambasada Babagana Kingibe, jigo a tafiyar APC ta kasa, kuma tsohon mataimakin Abiola a tikitin 1993, zabe da ake sa rai sun ci shi, lokacin mulkin Janar Babangida, ya fito ya karyata masu cewa wai yana neman takarar shugaban kasa a 2019.

A sanarwa da ya fitar a shafukan jaridu a yau juma'a, ya musanta masaniya a kan fastocinsa da ke ta yawo a manyan biranen kasar nan, inda ya danganta abin da zuki ta malle, da ma bata suna.

A cewar sanarwar dai, Kingibe, yace yana tare da shugaba Buhari a aikinsa na mulki, kuma yana tare dashi, kuma baya sansanar kujerarsa ko kadan, ko a 2019 ko a gaba.

Fastocin dai sun tayar wa da manyan jam'iyyun kasar nan tsimi, bayan da suka nuna kamar martani ne ga wasikar Obasanjo, kan lallai kar shugaba Buhari yayi takara a 2019.

DUBA WANNAN: Fulani na da ikon zama duk inda suke a kasar nan

Shi dai Kingibe, a baya, ya rasa irin wannan kujerar tasa a mulkin PDP, bayan da Ummaru Yar'aduwa ya kore shi yana tsaka da aiki, dawowarsa daga rashin lafiya, inda aka ce ya so yayi juyin mulkin cikin gida ya dora kansa mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng