Uwargidar El-Rufai ta feɗe biri har wutsiya dangane da matsalolin da matan Arewa ke fuskanta
Uwargidar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, Hajiya Hadiza Isma ta kaddamar da wani sabon littafi da ta rubuta don fayyace ire iren matsalolin da mata suke fuskanta a Arewacin Najeriya.
Duba da tsararren labarin ne yasa gwamnan ya bayyana Matar tasa a matsayin wata marubuciya da za ta shahara a nan gaba kadan, yace har sai ta ninka Wole Soyinka da Chinua Achebe wajen sharara a harkar rubuce rubuce.
KU KARANTA: Karanta sakon da laftanar janar Buratai ya aika ma shugaban kungiyar Boko Haram
Littafin mai taken ‘An Abundance of scorpion’ ya kunshi da sashi sashi guda 27, ana samunsa a babban birnin tarayya Abuja, da kuma jihar Kaduna a kan kudi naira 3000, kamar yadda Legit.ng ta binciko.
Jaridar The Cable ta ruwaito El-Rufai a yayin jawabinsa yana fadin “Ina alfahari da mata ta, kuma ina mata murna domin wannan shi ne abinda ta dade tana muradi, don haka ina ganin tamkar mafarkinya ya zama gaskiya kenan a yanzu, saboda muce ce mai tsananin fikira da basira.”
Wata masaniya kan harkokin rubuce rubuce da ta yi sharhi akan littafin, Ngozi Osu ta bayyana cewa littafin na duba ne ga juriya, karfin hali da kuma kyawawan halaye.
Shi kuwa mai gayya mai aiki, Tony Elumelu, shugaban bankin UBA ya baiwa marubuciyar kyautan naira miliyan 10 don kaddamar da littafin.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasiru El-Rufai ta yi Karin albashi ga Malaman jihar da kasha 32.5, kamar yadda kwamshinan Ilimi Jafaru Sani ya bayyana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng