Matakai 6 da Shugaba Buhari ya dauka domin warware rikicin Binuwai
Akasin yadda wasu sassan al'umma da kungiyoyi ke zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari bai dauki matakai domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar Binuwai ba, Fadar shugaban kasa ta bayyana matakai 6 da shugaban ya dauka tun barkewar rikcin a cikin wata wasika da ya aike ga shugaba Majalisar Dattawa.
Ga jerin abubuwan da shugaba Muhammadu Buhari ya lissafa;
1) A ranar 4 ga watan Janairu, na umurci Ministan Harkokin Cikin Gida da Sufeta Janar na Rundunar Yan Sanda su je garin na Binuwai domin gano abin da ya faru kana su kawo min rahoto.
2) A ranar 5 ga watan Janairu, Sufeta Janar na Yan Sanda ya kawo min rahoton abin da ke faruwa a kuma tuni na umurce shi da koma garin na Binuwai da zama
KU KARANTA: Majalisar Dattijai tana murna da tabbatarwar da kotu tayi mata na ikon kin amincewa da Magu
3) A ranar 8 ga watan Janairu, Ministan Harkokin Cikin Gida ya yi taro da Gwamnonin jihohin Adamawa, Neja, Taraba, Binuwai da Nasarawa tare da Direktan Hukumar Yan Sandan Farar Hula (DSS), Sufeta Janar na Yan Sanda, Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara har ma da wasu ruwa da tsaki a fanin tsaro.
4) A ranar 9 ga watan Janairu, Nayi taro da Gwamnan Jihar Binuwai, inda na bayyana masa cewa Hukumomin Tsaro sun kama wadansu da ake tuhuma da hannu cikin fitinar kuma ana cigaba da bincike domin tabbatar da tsaro a yankin.
5) A ranar 15 ga watan Janairu, Kamr yadda Gwamnan jihar Binuwai ya bukata, nayi taro da tawagar Dattawa daga jihar Binuwai inda muka tattauna kan matsalar kuma na kara tabbatar musu da kudiri na na kawo karshen rikicin.
6) A halin yanzu muna aiki tare da Gwamnonin Jihohin da rikicin ya shafa domin inganta tsaro da kuma binciko da hukunta wadanda ke da hannu cikin asasa fitinar.
Idan mai karatu bai manta ba, a kwanakin baya Legit.ng ta kawo muku rahotanni inda wasu kungiyoyi da mutane ke zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari bai mayar da hankali wajen kawo karshen rikicin ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng