‘Yan bindiga sun aika wani ‘dan kasuwa a Kudancin Kaduna lahira

‘Yan bindiga sun aika wani ‘dan kasuwa a Kudancin Kaduna lahira

- An kashe wani babban ‘dan siyasa a Kudancin kaduna

- ‘Yan bindiga ne su ka hallaka Moses Banka a Godogodo

- Bayan an harbe Banka babu wanda ya iya bin sahun su

Mun samu wani labari mai ban takaici cewa an kashe wani ‘Dan siyasa kuma 'dan kasuwa a Jihar Kaduna mai suna Moses Banka wanda ya fito daga Karamar Hukumar Sanga da ke Kudancin Jihar.

Moses Banka ‘dan siyasa ne kuma babban ‘dan kasuwa a Jihar Kaduna. Daily Independent ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga ne da ba a san su ba su ka kashe Banka a Kauyen Ankwa da ke cikin Masarautar Jema’a.

KU KARANTA: Majalisa na nema ta kawowa Buhari cikas wajen yaki da Boko Haram

Kantoman Yankin Alh. Yusuf Usman ya tabbatar da faruwar wannan mummunan abu ga manema labarai a jiya Alhamis. Alhaji Usman yace an kashe Banka ne cikin dare a ranar Laraba a gidan sa da ke kauyen Godogodo.

Wadannan ‘yan bindiga dai ba su kashe kowa ba lokacin da su ka shiga har dakin na sa a Garin Kafanchan. Marigayi Banka hamshakin manomin wakin suya ne a yankin kuma ‘dan kasuwa ne kuma mai gidan ‘Yan siyasar Yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng