An tsinci wasu gawarwakin mutane biyu a cikin birnin Abuja

An tsinci wasu gawarwakin mutane biyu a cikin birnin Abuja

- An gano wasu gawarwaki a cikin birnin Abuja

- An gano daya a Utako, daya kuma a Jabi

- Wani direba ya shaida wa majiyar mu faruwar lamarin

An samu gawarwakin mutane biyu a cikin birnin Abuja
An samu gawarwakin mutane biyu a cikin birnin Abuja

An gano gawar wasu mutane biyu a wurare daban – daban a cikin Abuja. An gano gawa daya a Utako, daya kuma a Jabi, duk a cikin birnin Abuja.

Wani direban taxi, da yake aiki a Utako Motor Park, ya ga daya daga cikin gawarwakin, inda yace sunan shi Wasi’u, wanda ya kasance dan asalin jihar Osun ne, direban ya tabbatar da cewar, marigayin shima direban taxi ne.

DUBA WANNAN: Kayi murabus kawai, inji majalisar wakilan jihar Bunuwai ke gaya wa Ministan tsaro

An gano gawar marigayi Wasi’u ne a cikin motar sa bayan rai yayi halin sa, ba da dadewa ba bayan sallar asuba ranar Alhamis. Oladipo ya shaidawa majiyar mu, cewar sun ga marigayin a cikin masallaci kafin ayi sallar asuba, ya kara da cewar lallai marigayin ya mutu ne bayan an idar da sallah ya dawo ciklin motar sa.

“Bayan mun idar da sallar asuba din, mun lura cewa motar sa tana nan a wurin da take, wato bai fita aiki ba. Don haka muka tafi mu duba shi, inda muka tarar shi a mace bakin shi duk da kumfa.”

A lokacin babu ko daya daga cikin shugabannin kungiyar direbobin ba ballantana mu samu Karin bayani, sai dai Oladipo ya ce an tafi da gawar ta sa jihar Osun. Babban jami’in ‘yan sanda na Utako, CSP Jimoh Gibenle, y ace ba a bayar da rahoto a tashar ba.

A daya bangaren kuma, an harbe wani mutum har lahira, a wurin wani wasan kwaikwayo na Hausa, a Jabi ranar laraban nan da ta wuce da daddare.

Da muka tuntube shi a waya Babban jami’in ‘yan sanda na unguwar CSP Danlami Yusufu, ya ce mutanen su suna bakin kokarin su domin bincike akan abinda ya faru. Inda ya aika da manema labarai ga babban ofis nasu na Abuja.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda na Abuja, Jesse Menzah, ya ce zai dawo ga wakilan mu, idan sun gama bincike akan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: