An sa Miliyan 50 ga duk wanda ya kamo wani Hatsabibi a Benuwe
- Gwamnan Benuwe Ortom ya sa kudi kan duk wanda ya kamo masa Gana
- Gana da mutanen sa sun addabi Yankin Benuwe da barna tun ba yau ba
- Yanzu haka za a bada kudi Naira Miliyan 50 ga wanda iya kawo kan Gana
Labari ya zo mana cewa Gwamnatin Jihar Benuwe na neman gawurtaccen mai laifin da ya addabi Jihar wanda aka fi sani da Gana. Kwamishinan yada labarai na Jihar Lawrence Onoka ke bayyana wannan. Gwamnatin Jihar ta dauki matakin ne jiya.
Gwamnatin Samuel Ortom ta kara kudin da ta sa na duk wanda ya kawo mata Gana. Yanzu haka Hukuma na neman Terwase Akwaza watau Gana ruwa a jallo. A da, an yi alkawarin Miliyan 10 ga duk wanda ya kamo wannan hatsabibi.
KU KARANTA: APC tayi watsi da sabuwar Kungiyar Obasanjo
Yanzu dai an kara wannan kudi zuwa Naira Miliyan 50 ga duk wanda ya iya kamo Gana a jiyan nan. Majalisar zartarwa na Jihar Benuwe ta bayyana wannan bayan taron da tayi na makon nan a Makurdi inji manema labarai na kasar nan.
Gana ya fitini Yankin Sankera da shi da Mukarraban sa. Gwamnati ta bada akwatin waya domin bada rahoto game da wannan fitinannen mai laifi. Haka kuma Gwamnan ya nemi Jami’an tsaro su kama duk wanda ya rufe lambar motar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng