Sakkawata sun kai kukansu gaban Sarkin Musulmi kan za’a yi musu mulkin kama karya
Daruruwan al’ummar kauyen Kucciyar lalle dake cikin karamar hukumar Bodinga ne suka dira fadar mai alfarma sarkin Musulmi bisa zargin karfa karfa da ake neman a yi musu game da dakacin kauyen.
Jama’an sun bukaci mai alfarma sarkin Musulmi ya shiga tsakaninsu da shugaban karamar hukumar Bodinga, bia yunkurin da yake yin a kakaba musu wani mutumi a matsayin dakaci, wanda suka ce bai gaji kujerar ba.
KU KARANTA: Tsohon babban hafsan rundunar Soja ruwa ya sulala ya mayar ma hukumar naira miliyan 600 da ya sata
Daily Trust ta ruwaito shugaban tawagar, Nasiru barade yana fadin cewa shugaban karamar hukumar su, Abubakar Dantsara tare da hadin bakin wani hakimi ne suke neman tayar da hankali a kauyensu, ta hanyar nada wani jigon jam’iyyar APC a matsayin dakacin su.
“Ba zamu yadda da nadin mutumin da suke neman kakaba mana ba, saboda ba dan garinmu bane, kuma ba dan sarautar bane, don haka bai gada ba.” Inji Barade.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Barade yana fadin shugaban hukumar Bodinga na nufin saka ma abokin siyasarsa ne saboda gudunmuwar da ya bashi a yayin yakin neman mukamin ciyaman, don haka suke rokon Sarkin Musulmi ya shiga maganan, ya dakatar da wannan dauki dora da ake naman yi musu.
“Muna kira da Sarkin Musulmi ya nada mana Sambo Barade, wanda shi ne dan marigayi tsohon Dakacin kauyen, kuma shine wanda jama’a ke kauna ya shugabance su.” Inji Baarade.
Sai dai shugaban karamar hukumar ta Bodinga ya musanta wannan zarge zarge, inda yace hakimin yankin tare da manyan masu rike da mukaman sarautun gargajiya ne suka zabo sabon Dakacin, kuma yace wannan zabe ya gudana ne a karkashin sa idon wakilin Sarkin Musulmi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng