Boko Haram tayi asarar mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya

Boko Haram tayi asarar mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya

- Boko Haram tayi asarar mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya

- Suma mayakan na Boko Haram sun samu nasarar kashe wasu mazauna garin na Madagali su 3

- Amma mun samu cewa ba su kashe soja ko daya ba

Labari mai dadin da muke samu daga majiyar mu na nuni ne da cewa sojoji da kuma mafarauta sun samu nasarar kashe wasu manyan mayakan kungiyar nan ta Boko Haram dake ci gaba da yaki da jami'an tsaro a garin Madagali, jihar Adamawa.

Boko Haram tayi asarar mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya
Boko Haram tayi asarar mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya

KU KARANTA: Yan shi'a sun kada 'yan sanda a kotun garin Sokoto

Haka nan ma mun kuma samu cewa mayakan na Boko Haram sun samu nasarar kashe wasu mazauna garin na Madagali su 3 a yayin harin da suka kai masu a jiyan.

Legit.ng ta samu a wani labarin kuma, a jiya Laraba da tsakar dare wasu 'yan bindiga dadi fataken dare suka afkawa wani kauye da ake kira da Kaguru dake a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna inda kuma suka kashe akalla mutane shidda.

Mun samu dai cewa 'yan bindigar da ake kyautata zaton barayin shanu ne sun far ma kauyen da tsakar dare inda suka yi ta harbe-harben bindiga a sama kafin daga bisani su fatattki mutanen kauyen duka.

Mun samu cewa daya daga cikin 'yan garin da lamarin ya auku a kan idon sa ya shaidawa majiyar mu cewa bayan 'yan kauyen duka sun tsere sai maharan suka rika shiga cikin gidajen su suna kwance dukkan shanun da suka mallaka suna tafiya da su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng