Kasar Rasha ta kausasa harshe akan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, ofishin jakadancin ƙasar Rasha ya caccaki gwamnatin ƙasar Amurka akan adawa tare da ƙiyayya da take nuna wa al'ummomin ƙasar ta.
Ƙasar ta Rasha ta gargaɗi gwamnatin shugaba Trump akan ɗabi'u marassa kamala da cancanta.
Wannan gargaɗi ya biyo bayan hana jakadan ƙasar Rasha shiga wata farfajiyar diplomasiyya mallakin ta dake ƙasar Amurka.
Cibiyar jakadancin ƙasar Rasha ta bayyana cewa, yunƙurin mataimakin sakataren tsaro a kan harkokin diplomasiyya, Michael Evanoff ya tashi a hofi, domin kuwa bai samu damar shiga ofishin su ba dake ƙasar Amurka duk da cewar lafiya ƙalau take sai dai rashin aminci daga bangaren gwamnatin Trump.
KARANTA KUMA: Manyan jiga-jigan jam'iyyun APC da PDP sun shirya goyon Obasanjo wajen kaddamar da sabuwar jam'iyya
Cibiyar ta ƙara da cewa, ba zai yiwu ta lamunci wannan cin fuska ba da wulaƙantaswa a sakamakon rashin kyawawan ɗabi'u na Trump.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng