Dalilai shida dake sa sauro cizon wasu mutane - Likiotci
- Binciken da wasu likitocin kimiyya suka gudanar ya sa sun gano mutanen da sauro yafi son cizo
- Mata masu ciki da masu shan giya suna cikin wadanda sauro yafi son shan jinin su
Kamar yadda mutane dayawa suka sani sauro yana daga cikin kananan kwari amma bala’in sa yafi yawa sosai.
Binciken da wasu likitoci kimiyya suka gudanar yasa sun gano dalilai shida dake sa sauro cizon wasu mutane.
Ga dalilin kamar haka
1. Sanya bakakken kaya ko kaya masu duhu a lokacin bacci
Bincike ya nuna a wasu lokutan sauro yana son duhu kuma yafi bibiyar mutane dake sanye da bakaken kaya ko kaya masu duhu a lokacin bacci..
KU KARANTA : Gwamnaonin Najeriya karnuka ne mara sa hakura - Ishaku Darius
2. Yanayin jinni ko nau’in sa
Wasu lokuta sauro yana bin yanayin jinin mutum wata kila nau’in jinin sa mai karfi ne ko kuma mara karfi.
3. Numafashi mai karfi lokacin bacci
Numafashi mai karfi a lokacin bacci yana janyo sauro zuwa jikin mai yin shi.
4. Rashin wanka da tsafta
Kamar yadda muka sani waje mara tsafta kamar kwata, bola, baka raba su da sauro, haka mutum Idan ya zama baya son wanka ko tsaftace jikin sa tabbas mayar da kansa abincin sauro.
5. Mace mai ciki
Sauro yana jindadin shan jinin mace mai ciki, dalilin haka yasa wasu lokuta Idan aka haifi yaro sai a samesa baida lafiya.
6. Mutum mai shan giya da kayan barasa
Sauro yana son giya da warin ta sannan kuma yana san jinin da giya ta shiga cikin sa, dalilin haka yasa sauro ke son cizon mutumin dake shan giya.
Allah kara muna lafiya, ya kuma karemu daga cututtuka manya da kanana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng