'Yan Majalisa sun gargadi Ministan babban Birnin Tarayya Abuja
- Wani Dan Majalisa ya gargadi Ministan Tarayya Abuja
- Hon. Agunsoye yace an bar cikin Garin Abuja cikin duhu
- An kuma koka da rashin ‘Yan Sanda a cikin Birnin Abuja
Majalisar Wakilan Tarayya ta koka da fama da ake yi da duhu a cikin babban Birnin Tarayyar kasar na Abuja inda su ka koka da cewa babu fitilu yanzu a kan hanya.
Wani Dan Majalisar kasar daga Jihar Legas ne ya kawo wannan maganar a wani zama da aka yi a Majalisar inda ya jawo hankalin Minista Muhammad Bello cewa babu haske a manyan titunan Birnin musamman a tsakiyar Garin.
KU KARANTA: Wani 'dan kasuwa ya kashe yar sa a Imo
Honarabul Rotimi Agunsoye na mazabar Kosofe a Legas ya nemi Ministan na Abuja ya sa fitilu a kan duk wata gada sannan kuma an nemi a sa fitilu masu haske a bakin titi da kuma saman manyan allunan da ke cikin Birnin.
Majalisar ta kuma koka game da sha'anin tsaro inda tace yanzu babu wasu 'Yan Sanda da za a samu a gefen hanya da kasan gada wanda hakan na da hadarin kuma aka nemi Sufetan 'Yan Sanda na kasar ya dauki mataki da wuri.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng