Manyan ‘Yan PDP sun yi ca a kan Gwama Ayo Fayose

Manyan ‘Yan PDP sun yi ca a kan Gwama Ayo Fayose

- Fayose na kokarin nada Mataimakin sa ya gaje shi

- Wasu ‘Yan Jam’iyyar ba su amince da wannan ba

- Gwamnan na Ekiti yace ba zai janye shirin na sa ba

Tsohon mai magana da yawun bakin Jam’iyyar adawa ta PDP Dayo Adeyeye yayi kaca-kaca da Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose inda yace Gwamnan na kokarin hada kai da ‘Yan adawa.

Ayo Fayose ya hada kai da ‘yan adawar PDP a Jihar Ekiti inji Adeyeye wanda yana cikin masu neman takarar Gwamnan Jihar. Gwamna Fayose ya zabi Mataimakin sa ya gaje sa a mulkin Jihar inda ya nemi wanda ba su yarda ba su bar PDP.

KU KARANTA: Za a nada wasu Kwamishinoni a Jihar Bauchi

Daga cikin masu neman kujerar Gwamnan akwai Tsohon mai magana da bakin PDP Adeyeye. Shi dai Gwamna Fayose yana kokarin hana sauran ‘Yan PDP sakat inda ya matsa cewa sai ya nada Farfesa Kolapo Olusola matsayin ‘dan takarar PDP.

Sauran masu neman kujerar Gwamnan Jihar na Ekiti itin Sanata Abiodun Olujimi da wani tsohon Jakadan kasar ba su yarda da shirin na Gwamna Fayose ba sun kuma nemi a sa baki. Sai dai Gwamnan yace ba zai janye wannan yunkurin na sa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: