Ana rikicin kan iyaka tsakanin jihohin Yobe, Gombe da Bauchi
- Ana rikicin kan iyaka tsakanin jihohin Yobe, Gombe da Bauchi
- Jihohin a jiya Talata sun yi wani zaman sasanci domin lalubo hanyoyin da za su sasanta kansu
- Hukumar shata kan iyakoki ta gwamnatin tarayya ma ta halarci zaman sulhun da aka gudanar
Gwamnatocin jihohin Bauchi, Gombe da kuma Yobe a jiya Talata sun yi wani zaman sasanci domin lalubo hanyoyin da za su sasanta kansu game da dambarwar rikicin kan iyaka da suke fama da ita a cikin ruwan sanyi.
KU KARANTA: Kungiyoyi 200 sun tsayar da Buhari takara a 2019
Mun samu dai cewa gwamnatin jihar Yobe ce ta kirawo taron tsakanin jihohin takwarorin ta sannan kuma hukumar shata kan iyakoki ta gwamnatin tarayya ma ta halarci zaman sulhun da aka gudanar a jihar.
Legit.ng ta samu dai cewa Gwamnan jihar ta Yobe mai masaukin baki ya bayyana cewa sun kudurin bin wannan hanyar ne domin magance rikicin domin daga karshe jihohin su samu amincewa da dukkan hukuncin da aka yanke sannan kuma dangantar su ta cigaba.
A wani labarin kuma, Bankin nan na sana'oi da kasuwanci mallakin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ya rarraba akalla Naira 18 biliyan daga cikin Naira 20 biliyan ga kanana da kuma manyan masana'antu da aka ware a jihar Oyo.
Shugaban bankin dai mai suna Mista Olukayode Pitan shine ya sanar da hakan yayin da ya jagoranci tawagar bakin zuwa wata ziyarar bangirma da suka kai wa gwamnan jihar ta Oyo a ofishin sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng