Yadda wani Soja da dansa suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da Boko Haram

Yadda wani Soja da dansa suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da Boko Haram

- Manjo Kanoma na cikin jaruman sojojin da suka sadaukar da rayuwar su wajen yaki da Boko Haram

- Kafin rasuwar sa, Manjo Kanoma ya koka kan yadda hafsoshin sojojin ke fama da karancin kayan yaki alhalin 'yan siyasa na wadaka da kudi zamanin tsohon shuigaba Jonathan

- Bayan rasuwar sa, dan sa mai suna Zeeyan ya bi sahun mahaifinsa inda ya shiga aikin sojan amma shima Allah ya masa rasuwa wajen yaki da yan ta'addan

Shi dai wannan jarumin Sojan mai suna Manjo Kanoma ya shiga aikin soja ne a matsayin karamin jami'i amma saboda basira da jamrumtaka sa ya sa akayi masa karin girma a 2014 zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Manjo Kanoma ya hallarci kusan dukan aiyukan kwantar da tarzoma da gamayyar sojojin kasashen Afirka ta yamma (ECOMOG) suka gudanar a kasashen da ke yankin Afirka ta Yamma.

Yadda wani Soja da dansa suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da Boko Haram
Yadda wani Soja da dansa suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaki da Boko Haram

A shekarar 1990's, An harbi Manjo Kanoma a yayin da suke aikin kwantar da tarzoma a yankin Darfur amma ya murmure daga baya. Jim kadan bayan dawowar sa daga Dafur ne aka tura shi yankin Arewa ta Gabas domin yaki da yan ta'adda Boko Haram.

KU KARANTA: Gobara tayi sandiyar mutuwar dalibin makarantar Sakandare a Sakkwato

A bawa Manjo Kanoma jagorancin wata Bataliyar da ke fama da karancin makamai da sauran kayayakin yaki, amma hakan bai hana shi gudanar da aikin sa yadda a dace ba.

Akwai lokacin da ya aike da sako inda ya ce "Akwai irin halin da mutum idan ya tsinci kansa zai sa ya zama dan gwagwarmaya, akwai irin tabarbarewar da al'amura zasuyi da zai sa mutum ya dauki mataki ko da kuwa hakan zai yi sanadiyar ajalin sa"

A wannan lokacin ne yan siyasa ke ta wadaka da kudin da ya kamata a siyo wa sojojin makamai a karkashin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan alhali sojojin na yaki da yan ta'addar da ke da makamai manya-manya.

Jim kadan bayan wannan rubutun ne yan Boko Haram suka sami galaba a kansa da rundunar sa. Shekau biyu bayan rasuwar sa, Dan sa mai suna Zeeyan Kanoma ya bi sahun Mahaifinsa inda ya shiga aikin sojan domin ya bayar da gudunmwarsa wajen yaki da yan ta'addar da suka saka kasar mu a gaba.

Zeeyan na nuna jaramtaka sosai a filin daga kamar yadda mahaifinsa ya yi, sai dai ranar Juma'ar makon da ta wuce shima Zeeyan ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda dan uwan marigayi Manjo Kanoma, Mamman Bashir Kanoma ya rubuta a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164