Sojojin Najeriya sun fara gina titi daga cikin Gari zuwa Dajin Sambisa
- Sojojin Najeriya na kokarin gina hanyoyi zuwa cikin Dajin Sambisa
- Ana kuma kokarin gyara wasu hanyoyin da ke shiga cikin Sambisa
- A baya dai Sojojin kasar sun maida kungurmin Dajin wajen atisaye
Mun samu labari cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun fara gina titi daga cikin Garuruwan Jihar Borno zuwa Dajin Sambisa inda a da ya zama wani babban matattara na ‘Yan ta’addan Boko Haram.
Sojin Najeriyar na kokarin gina hanya ne har zuwa kungurmin Dajin na Sambisa da yayi fice da ‘Yan Boko Haram. Rundunar Sojin kasar na kokarin ganin an maida Dajin inda za a iya zama kuma har a horar da Jami’an Sojoji.
KU KARANTA: An shirya wani taro domin 'yan sara-suka a cikin Zariya
Yanzu haka an soma aiki a cikin Dajin inda ake kokarin gyara hanyoyin da su kai ga Dajin. Daga ciki akwai hanyar Gwoza zuwa Yemteke har Bitta zuwa Tokumbere, Daga nan ne dai za bulla har cikin tsakiyar Dajin na Sambisa.
Kuma bayan nan akwai hanyar da ake yi daga Gwoza zuwa Garin Yamteke har Garin na Bitta. An kuma yi nisa wajen hada wannan hanyoyi a kan iyaka. Sojojin kasar sun soma yin atisaye da sauran ayyuka dama can a cikin Dajin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng