Hotunan dan majalisa mai tsawatarwa a majalisar wakilai yayin da yake jagorantar matasa ɗauke da muggan makamai
Al’amuran siyasa na cigaba da zafafa a jihar Kano tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwasoya sanya ranar 30 ga watan Janairu a matsayin ranar da zai ziyarci jihar.
Amma abinka da yan uba, kuma da yake tsohon gwamnan sun raba gari da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sai gwamna Ganduje shi ma ya sanya ranar 30 ga watan a matsayin ranar da zai shirya wani gangami, wanda hakan ya sanya Kwankwaso janye ziyarar ta sa.
KU KARANTA: Jarumar Kannywood ta miƙa kokon soyayyarta ga wani Saurayi dan Fim
Sai dai Legit.ng ta ruwaito duk da tsohon gwamnan jihar ya janye ziyarar ta sa, amma sai da magoya bayan gwamnan suka dira wajen yin gangamin siyasar dauke da makamai, zagaye da kauraye da yan daba.
An hangi mai tsawatarwa na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa a yayin taron yana jagorantar wasu gungun kauraye da yan daba, haka zalika shi ma wani dan majalisar dokokin jihar Kano, Abubakar Zakari an hange shi yana dauke da makamai, tare da yin shigar yan tauri.
Wannan ne ya sanya masu lura da al’amuran yau da kullum suka yi sharhin cewa da ace sanata Kwankwaso ya shiga jihar Kano a yau, da kuwa an yi kare jinni biri jinni a tsakanin masoya Ganduje da na Kwankwaso.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng