Tsugunni bata kare ba: An kai ma jama’a hari a jihar Kano a hanyar zuwa taron Gandujiyya
Wani rahoto daga jaridar Rariya ya tabbatar da cewa wasu matasa dauke da muggan makamai sun kai harin mai kan uwa da wabi a jihar Kano, a yayin da ake tafiya zuwa taron Gandujiyya.
Wannan lamari ya faru ne a daidai kusa da gidan mai na A.A Rano dake unguwar Na’ibawa, a yayin da matasa da masu tarin yawa da suke kan hanyar tafiya taron na Gandujiyya da ke gudana a kwanan Dangora.
KU KARANTA: Tabdijam: An samu shugaban kasa guda 2 biyo bayan rantsar da madugun yan adawa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an samu mutane da suka jikkata, daga cikinsu akwai wani da aka dauki hotonsa kansa duk jinni, haka zalika an hangi matasan sun raka sauran jama’a a guje.
Idan za’a tuna dai, a jiya ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dage ziyarar da yayi niyyar kaiwa jihar Kano, bayan gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya sanya na shi taron a kwanar Dangora, duk a ranar daya.
A wani labarin kuma, wani dan darikar Kwankwasiya ya yi asarar motarsa da Filinsa, biyo bayan caca da yayi akan cewa lallai Kwankwaso zai shiga Kano a ranar 30 ga watan Janairu, amma bai samu sa'a ba, sai Kwankwaso ya dage tafiyar ta sa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng