Yaki da jahilci: An sanya fursunonin Najeriya a jami'a

Yaki da jahilci: An sanya fursunonin Najeriya a jami'a

- Da yawan fursuna a kasar nan sukan koma ruwa saboda rashin iya katabus da rayuwarsu

- An maida wasu fursunonin kamar bayi, musamman ma ganin yaran talakawa ne

- Gwamnati na kokarin inganta rayuwarsu bayan sijin

Yaki da jahilci: An sanya fursunonin Najeriya a jami'a
Yaki da jahilci: An sanya fursunonin Najeriya a jami'a

Gwamnatin Najeriya na kokarin habaka da inganta rayuwa ta ffursunoninta miliyoyi da ke zaune don jiran sharia da ma sama musu aikin yi da guraben karatu a budaddiyar jami'a ta NOUN.

Karatun fursunonin dai shine irin shi na farko a tarihin kasar nan, domin an ffi samun marasa ilimi a kurkuku, an kuma samun talakawa a abubuwa da suka danganci laifi,

An bai wa fursunoni 430 guraben karatun digiri daban-daban a jami'ar karatu daga gida ta Najeriya (NOUN) domin su inganta rayuwarsu.

An kuma sallami wasu fursunonin 951 bayan da wasu masu ruwa da tsaki kan gyara ga gidajen yari suka tallafa musu.

A cikinsu akwai fursunoni uku da suke dab da kammala karatun digirinsu na uku a wasu jami'o'in Najeriya.

DUBA WANNAN: George Weah ya yankewa kansa albashi

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta najeriya Mista Francis Enebore ne ya bayyana wannan a Abuja yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai.

Ya kuma sanar da wani taro da babban daraktan hukumar gyara ga gidajen yari na kasa, Dr. Uju Agomoh ya halarta cewa an sallami fursunoni 951 bayan da suka cika dukkan ka'idojin da aka gindaya masu

Da yawa dai daga fursunan kasar nan bassu da wata rayuwa, sai fa neman na tuwo wanda kan maishe su laiukan da suka kawo su da farko.

Akwai miliyoyin mutane da ke zaman jiran sharia a kurkuku a kasar nan, kuma akan manta ma da zamansu na shekaru.

An samo labarin ne daga BBCHAUSA

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng