Fasa zuwa Kano da Kwankwaso ya yi, ya bar baya da ƙura, wani Matashi ya yi asarar Filinsa da Motarsa
A sakamakon dage shiga jihar Kano da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi a ranar Litinin 29 ga watan Janairu, hakan ya bar baya da kura a tsakanin magoya bayansa.
A cikin wani zantawa da BBC Hausa ta yi da wasu magoya bayan Kwankwaso na hakika, wani daga cikinsu mai suna Honorabula Gamboliya Jahir ya tafka asara, a sakamakon caca da yayi dangane da ziyarar Kwankwason.
KU KARANTA:
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gamboliya ya yi alkawarin kyautar da Motarsa da Filinsa, matukar jagoran Kwankwasiyya ya fasa shiga jihar Kano a ranar 30 ga watan Janairu, kamar yadda ya shirya a baya, inda yace ya tabbatar Kwankwaso baya magana biyu.
“Ni ban ji komai ba, dama abubuwan nan a Duniya na same su, kuma a Duniya zan bar su.” Inji Honorabul Gamboliya Jahir.
Ita kuwa wata matashiyar yar siyasa da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar ma majiyar mu lallai sai sun yi taro a ranar Litinin ko ba Kwankwaso, inda tace zama cikin APC ba dole bane, kuma idan Kwankwaso ya ga dama ya tsaya, ita kam tayi tafiyarta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng