Tinubu ya jaddada mubaya’a ga shugaba Buhari: Bana karuwancin siyasa, ina tare da Buhari ɗari bisa ɗari
Jagoran jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu ya jaddada goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don ganin ya ciyar da Najeriya gaba, kamar yadda shafin labaran jam’iyyar APC ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito jagoran, kuma tsohon gwamnan jihar Legas yana fadin cewar ba shi da wani shakku ko kadan game da shugaba Buhari, kuma zai cigaba da dafe masa har ya kai Najeriya tudun mun tsira.
KU KARANTA: Wata Mata da farkanta sun kashe Mijinta bayan ya kama su haihuwar uwarsu suna lalata da juna
“A tsarin mu bama yin karuwanci a siyasa, don haka zan cigaba da zama da jam’iyyar APC tare da ba da goyon baya ga shugaba Buhari da dadi, da ba dadi, duk runsti duk wuya.” Inji shi.
Tinubu ya bayyana haka ne duba da wasu rahotanni da ake yadawa na cewa wai akwai kishin kishin jagoran bai zai mara ma Buhari baya ba, musamma duba da karatowar zabukan 2019.
Sai dai dukkanin bangarorin guda biyu sun sha musanta wannan jita jita, haka zalika a koda yaushe suna kokarin tabbatar da kyakkyawan alaka dake tsakaninsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng