Akwai yiwuwar wasu kamfanoni 6 zasu rasa lasisin aikin su, inji Hukumar NCC
- Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa NCC ta ce wasu Kamfanoni 6 na gab da rasa lasisin aikin su
- Hukumar NCC din ta same su da laifin aikata wata haramtaciyar dabarar bawa wasu abokan hulda damar maganan da lambobin sirri tsakanin kasa da kasa
- Hukumar ta ce hakan ya sabawa wa doka domin ana amfani dashi wajen leken asiri na kasa da kuma cinikayyar haramtattun ababe
Hukumar da ke kula da Kamfanonin Sadarwa NCC ta ce duk kamfanonin da aka samu da laifin sirrinta lambobin kira na kasashen waje za su gamu da fushin hukuma.
A wata sanarwa da ya bayar ranar Talata, Direktan hulda da al'umnma na hukumar, Tony Ojobo ya ce, cikin makon da zamu shiga, hukumar zata kwace lasisi ko kuma dakatar da wasu kamfanonin sadarwan da aka samu da hannu wajen aikata laifin.
Shi dai sirrinta lamabobi wani dabara ne da ake amfani dashi a fanin sadarwa domin boye lambobin wayar masu saye da sayarwa, ana amfani da wata lamabar waya ta musamman ne na wucin gadi idan an gama kiran sai ayi watsi dashi.
KU KARANTA: Sojojin Saman Najeriya sunyi sanadiyar mutuwar 'yan Najeriya da dama - Amnesty International
Kamfanonin da ake tuhumar su da aikata wannan laifin sun hada da Medallion Communications Ltd, Interconnect Cleaning House Nig. Ltd, Niconnx Communication Ltd, Breeze Micro Ltd, Solid Interconnectivity da kuma Exchange Telecommunications Ltd.
Kamar yadda Kamfanin Dillanci Labarai NAN ta ruwaito, an bawa kamfanonin da ake tuhuma dama su kare kansu, bayan hakan kuma duk wanda laifin ya tabbata a kansu za u fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanadadomin hatsarin da abin ta ke dashi kan sirrin kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng