Sha’anin wutar lantarki yana sama yana kasa a Najeriya
- Ana ta fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya a shekarar nan
- Gidan wutan na ta samun matsala bini-bini a cikin kwanakin nan
- Sai Gwamnati ta tashi tsaye wajen shawo karshen wannan matsalar
Mun samu labari cewa yanzu haka wutar lantarkin Najeriya na ta samun matsala a cikin ‘yan kwanakin nan. A makon nan sai da gidan wutan kasar ya samu matsala kusan sau 6. Dole sai Gwamnati tayi kokari wajen kawo karshen wannan matsalar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa daga farkon shekarar nan zuwa karshen makon farko sai dai asalin gidan wuta na kasar ya dauke har sau 6 a cikin ‘yan kwanaki kadan. Karfun wutar kasar sai dai ya ragu daga megawatts 36675 zuwa megawatts 5 kacal.
KU KARANTA: An damke wasu za su haura da fetur ketare
Tun a ranar 1 ga Watan Junairun bana abubuwan su ka fara tabarbarewa. Bayan kwanaki 2 kuma dai aka karu samun wannan matsala. Haka-zalika a Ranar 5 ga wata ne kuma karfin wutan yayi kasa daga sama da megawatts 2600 zuwa megawatts 107.
A ranar 6, 7 da kuma 8 dai ba a samu sukuni ba inda a kowace rana sai abin ya kara tabarbarewa. A ranar 8 ga wata sai da ta kai karfin wutar da aka samu a kaf Najeriya bai wuce megawatts 72 ba. Ana yawan samun matsalar ne daga Legas zuwa Benin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng