Duniyar bakin mutum tana bukatar mutanen Najeriya domin ta cigaba - Aregbesola
- Gwamnan Jihar Osun Aregbesola ya nemi ‘Yan Najeriya su tashi tsaye
- Aregbosola yace dole mutane fa su nemi sana’a domin samun na abinci
- Gwamna Aregbesola yayi kira ga Jami’an tsaro su samar da zaman lafiya
Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbosola ya bayyana abin da ya sa bakin mutum ba zai taba rabuwa da Talauci ba. A cewar sa dai sai ‘Yan Kasar Najeriya sun yi da gaske wajen gyara Afrika baki da yam ba ma iyaka kasar su ba.
Gwamna Rauf Aregbesola ya nemi mutanen kasar nan sun tashi tsaye domin jagorantar Duniya bakin mutum baki daya. Gwamnan ya bayyana wannan ne a wajen wani bikin cika shekara 65 na wani babban Farfesan tarihi Toyin Falola a Garin Ibadan.
KU KARANTA: Zalunci ne hana ni zuwa Jihar Kano – Sanata Rabi’u Kwankwaso
Aregbsola a takardar da ya gabatar ya bayyanawa cewa an san ‘Yan Najeriya da kokari a Duniya baki daya. Gwamnan yace idan mutane miliyan 50 da za su zage da neman abinci ta hanyar sana’o’i, to za a samu sama da Tiriliyan 1 da rabi na yawo a kasar.
A cewar Gwamnan Duniya ta canza don haka Talakawan gari ne za su tashi su nemi abin yi inda kuma Gwamnati za ta dafa masu da abubuwan more rayuwa. Gwamnan ya kara da cewa ba a taba samun cigaba sai da zaman lafiya ganin yadda ake fama da harkar tsaro.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng