Dangote ya gina makarantan kasuwanci na kimanin N1.2bn ma jami’ar Bayero
Babban hamshakin maikudi kuma attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya gina babban makarantan kasuwanci kyauta ga jami’ar Bayero da ke jihar Kano domin koyar da kasuwanci da zai karfafa tattalin arzikin Najeriya.
Wannan gini dai an kamala gina ginata kuma za’a mikawa shugabancin jami’ar watan gobe. Masu sharhi sun bayyana cewa ginin ya amsa sunan gini kuma shine irinsa na farko a yankin Arewacin Najeriya.
Za’a tuna cewa Alhaji Aliko Dangote na gina irin wannan makaranta na kasuwanci a jami’ar Ibadan kuma za’a kaddamar da shi ba da dadewa ba.
Makarantun wanda gidauniyar Dangote ke ginawa game da cewar shugaban kamfanin Dangote na cikin gudunmuwar ta na karfafawa matasa dogaro da kai da ilimi a fannin kasuwanci.
Ya bayyana cewa halin da Najeriya ke ciki a yau, ya zama wajibi a koma kasuwanci da ilimi da kuma dogaro da kai musamman a aji biyu na karatun jami’a.
KU KARANTA: Kwankwaso ya nuna dattaku da ya dage zuwa Kano sai wani lokaci - Masana
Makarantan na cikin jami’ar Bayero ne, ta kunshi ajujuwa, dakunan taro, ofishoshi, dakunan karatu, na’urar sanyaya yanayi, da sauran su.
Shugaban makarantan, Farfesa Murtala Sagagi, a jawabin nuna godiyarsa ga Alh Dangote, y ace babu makarantan kasuwanci a jami’ar kafin yanzu.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng