Boko Haram: ‘Yan ta’adda ba su ji da dadi ba a Dajin Sambisa
- Sojojin sama sun kai hari ga ‘Yan Boko Haram a Sambisa
- An yi nasarar kashe ‘Yan ta’adda a harin da aka kai yau
- An kuma dace da tarwatsa kayan makaman ‘Yan ta’addan
Dazu mu ke jin cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram ba su ji da dadi ba a Sambisa. Har yanzu Rundunar Sojin kasar na kokarin ganin bayan ‘Yan Boko Haram da ke Arewa maso gabashin kasar inda ake kai wasu hare-hare na musamman a Dajin Sambisa.
Kawo yanzu dai mun ji cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram na kokarin tserewa daga Dajin Sambisa. Sojojin saman kasar dai sun bi su da ruwan wuta domin lallasa ragowar ‘Yan ta’addan da ke cikin Dajin na Sambisa a yau dinnan a wani hari na sama.
KU KARANTA: Masu fama da cutar kanjamau a haihuwa ya karu
Wani Babban Jami’in Sojojin sama na kasar Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ya bayyana cewa Sojojin su sun koyawa ‘Yan Boko Haram da ke makale a Sambisa hankali inda aka rusa ‘Yan ta’addan yayin da su ke kokarin tserewa daga dajin.
Sojojin saman Najeriya sun yi wa ‘Yan Boko Haram din aman wuta ne a lokacin da su ke hanyar su ta zuwa Garin Parisu inda su ke neman fakewa. Sojojin sun tarwatsa ‘Yan Boko Haram da kayan makaman da su ke rike da shi inda wasu su ka tsere.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng