Wasikar Buhari: Wani Minista yayi kaca-kaca da Obasanjo
da- Ministan sadarwa yayi kaca-kaca da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo
- Shitu yace Obasanjo bai da damar ya fadawa Buhari abin da zai yi a 2019
- Ministan yace ya kamata a fadawa Obasanjo irin kokarin Gwamnatin nan
Ministan sadarwa na Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Mista Adebayor Shittu ya soki tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo game da wasikar sa ta kwanaki ga Shugaban kasa.
Adebayor Shittu yace tsohon Shugaban kasar bai da hurumin hana Shugaba Buhari tsayawa takara a zabe mai zuwa. Shittu ya kuma nemi Jama’a su bayyanawa Obasanjo irin kokarin wannan Gwamnatin ta Shugaban kasa Buhari.
KU KARANTA: IGP: Kotu ta gargadi wani Sanatan Najeriya
Shittu ya fadawa manema labarai a fadar Gwamnatin kasar a Birnin Tarayya Abuja cewa Obasanjo yana da damar ya fadi ra’ayin sa amma fa babu dalilin yace Shugaba Buhari bai dace ya nemi ya zarce ba a kan kujerar Shugaban kasa.
Ministan kasar yace babu Gwamnatin da tsohon Shugaban kasar bai suka ba. Sai dai tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya daure Obasanjo a mulkin sa kafin a je a ko ina inji Ministan na sadarwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng