Ya nemi kotu ta raba aurensu saboda matar sa na amfani da al'aurar ta domin yin tsinuwa
- Wani Fasto a cocin Pentecostal ya nemi wata kotu dake Igando a Legas ta raba aurensa da matar sa saboda tana amfani da al'aurar ta domin tsine masa
- Ya kuma fada wa Kotu cewa matar tasa ta ishe shi da fitina hakan yasa baya sha'awar auren
- Matar ta karyata dukkan zargin da yayi mata, hasali ma ta ce shi ne ya gudu ya bar ta da dawainiyar yara
A takardar da ya mikawa kotu, Fasto Bernard Towoju, dan shekaru 53 a duniya, ya shaidawa kotu cewar ba zai iya cigaba da zama da matar da za ta yi zigidir sannan take zagaya gidata tana ambaton al'aurar ta tana tsine masa ba.
Towoju, mai shekaru 53, ya ce masifar matar sa tayi yawa, har ta kai ga ya gaji da zuwa ofishin 'yan sanda saboda yawan fadan da suke yi. A cewar Towoju, matar sa, Abosede, bata jin magana, ga rashin kunya da masifa kamar karya.
DUBA WANNAN: Sayar da kadarorin gwamnati: Wata kungiya ta bukaci gwamnati ta binciki Obasanjo
Saidai da take magana a gaban kotun, Abosede, ta musanta zargin da mijin nata ke yi mata tare a shaidawa kotu cewar 'yan tsibbu ke fadawa mijin cewar ita ce ta saka al'amuransa basa samun cigaba.
Kazalika Abosede, mai shekaru 46, ta fadawa kotun cewar mijin nata ya gudu ya barta da dawainiyar yaransu har na tsawon shekaru goma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng