Wata Mata da farkanta sun kashe Mijinta bayan ya kama su haihuwar uwarsu suna lalata da juna
Wani Maigida mai suna Ukechukwu Okeke ya gamu da ajalinsa a hannun Uwargidarsa a lokacin da ya kama ta a halin turmi da tabarya tare da wani yaron shagonsa, rahoton Rariya.
Wannan aika aika ya faru ne a kasar Kamaru, inda ma’auratan ke zaune suna harkokin kasuwanci, inda bayan wani dan loakci sai Maigidan ya fara ganin wasu take take daga matarsa, wanda bai saba gani ba, kuma bai gane ba.
KU KARANTA: Ana yi ma wata budurwa da ta musulunta a jihar Imo barazanar kasheta (Hotuna)
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mijin na zargin Matarsa, Chinenye na aikata badala da yaron shagonsa ne a cikin gidansu, haka ne ya sa ya kafa tarko da nufin tabbatar da zarginsa, ai kuwa aka yi sa’a Ugochukwu ya kama matar tasa da yaro shagon nasa kamar yadda yake zargi.
Ganin asirinsu ya tonu ne, sai suka diran ma Mijin, suka yi masa rubdugu, suka lakada masa dan bazan duka har sai da yace ga garinku nan, ya fadi matacce, ba tare da bata lokaci ba suka dauke shi cikin bargo suka saka shi a cikin Mota, da nufin jefar da gawar tasa.
Abinka da Alhaki, wani jami’in dansandan kasar Kamaru ya lura da alamun jini jinni na fita daga cikin motar a lokacin da ya dakatar da su a wani shingen binciken jami’an Yansanda, nan da nan kuwa Yansandan suka daka musu wawa, inda a yanzu haka suna hannu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng