Karin Haske Akan Batun Albashi a Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi
- Gwamnatin jihar Bauchi ta yi fashin baki kan batun albashin ma'aikatan jihar
- An cire N1000 daga kudin albashinsu ba tare da bayani ba
Gwamnatin jihar Bauchi ta yi fashin baki a kan korafe-korafen da ma'aikatan jihar jeyi bisa ga cire wani kaso na albshinsu na wata.
Jaridar Legit.ng ta samu wannan labari ne daga jawabin mataimaki na musamman ga Mai Girma Gwamnan Jahar Bauchi a fannin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar inda yace:
"Daga jiya zuwa yau mun samu korafe-korafe da dama daga jama'a inda suka ce an cire musu kudi ba tare da sanin su ba.
Gaskiyar magana shine, kudin da aka cire wa kowani ma'aikaci a Jahar Bauchi an cire ne domin yin katin shedan aiki na zamani mai dauke da cikakkun bayanai akan kowani ma'aikaci. Hakan zai taimaka wurin tsaftace hanyar gudanar da duk wani al'amari da ya shafi ma'aikata.
Wannan abu da aka yi, an yi tare da cikakken sanin ko wani ma'aikaci. Kungiyoyin kwadago gaba daya na Jahar Bauchi sun aminta da wannan tsari kuma sun ja hankalin mutanen su akan amfanin wannan katin sheda na musamman.
Kudin wannan kati Naira dubu daya ne. Amma kasancewar gwamnatin Mai Girma Gwamna Mohammed A. Abubakar mai tausayi ce, sai aka yanke shawarar cire Naira Dari Biyar kacal sau biyu (wato watan daya da watan biyu) maimakon a dauki kudin lokaci guda, don gudun kada a uzzura wa kowa.
Hakika Gwamnatin Jahar Bauchi karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Mohammed A. Abubakar gwamnati ce ta ma'aikata kuma mai kishin su.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za tayi amfani da karfin soji wajen kawo karshen rikicin makiyaya
Jahar Bauchi tana daya daga cikin Jahohi kalilan da ke iya biyan albashin ma'aikata cikakke kuma akan lokaci a fadin tarayyar Kasar nan. Haka kuma babu bashin albashi ko na wata guda akan gwamnati. Misali, albashin wannan watan an fara biya ne tun ranar 25 ga wata. Haka ma sauran watannin baya.
Muna kira ga Jama'ar Jahar Bauchi masu karamci da suyi watsi da duk wani jita-jita da ake yadawa don ganin an bakanta wannan gwamnati mai kishin ma'aikata.
A karshe, a madadin gwamnati ina mika godiya ta musamman ga daukacin al'ummar Jahar Bauchi domin irin adduoi da fatan alheri da suke mana. Ubangiji Allah Ya bamu sa'a da nasara."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng