Trump ya ce Amurka tana matukar girmama nahiyan Afrika a wasikar da ya rubutawa kungiyar AU
- Shugaban kasar Amurka ya aikawa kungiyar gamayyar Nahiyan Afriak AU wasika
- Donald Trump ya karyata zargin kiran mutanen Afrika kaskantattu
Shugaban kasar Amurka, Donald Teump, ya ce Amurka tana matukar girmama nahiyan Afrika a wata wasika da ya aikawa kungiyar gamayyar ksashen Afrika AU.
Wasikar yazo ne mako daya, bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya furta wasu kalaman batanci game da mutanen Afrika a lokacin da yake gudanar da wata taro da ‘yan majalissar kasar sa.
An zargi Donald Trump da kiran mutanen Afrika kaskantattun mutane a lokacin taron, wanda wannan al’amari janyo Donald Trump suka daga kasashe daban-daban.
KU KARANTA : Hukumar EFCC ta damke wani babban jami'in gidan kaso bisa zargin ba Patience Jonathan kwangilar naira miliyan N300
Amma Donald ya karyata zargin furta wadanan kalamai, inda yace kasar Amurka tana matukar girmama mutanen Afrika, kuma kyakywar alaka dake tsakanin kasar Amruka da nahiyar Afrika ba za ta taba gushewa ba a cikin wasikar da ya rubuta.
Ba a fito fili da wasikar ba amma daya daga cikin tawagar Amurka da suka halarci taron kungiyar AU, Chris Meade ya tabbatar da aika wasikar
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng