Mahaifiyata nake baiwa ajiyan bindiguna – Inji wani ƙasurgumi mai garkuwa da mutane

Mahaifiyata nake baiwa ajiyan bindiguna – Inji wani ƙasurgumi mai garkuwa da mutane

Wani kasurgumin dan fashi da makami, mai satar shanu, kuma mai garkuwa da mutane da ya shiga hannu a jihar Kaduna ya shaida ma manema labaru yadda Uwarsa ke taya shi aiki.

Dan fashin mai suna Ibrahim Umar, wanda aka fi sani da suna Sani-Da-Oro ya bayyana haka ne yayin da yake tona asirin yadda yake aikinsa, inda yace uwarsa da surukinsa yake baiwa ajiyan bindigunsa don gudun kada a kama shi da su.

KU KARANTA: Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna

Rariya ta ruwaito shi yana fadin: “Na ajiye sauran bindiguna a wajen uwata da surukina, kuma a baya mun amshi miliyoyin kudade daga hannu mutanen da muka yi garkuwa da su, amma a yanzu haka bani da naira hamsin.

Mahaifiyata nake baiwa ajiyan bindiguna – Inji wani ƙasurgumi mai garkuwa da mutane
Ibrahim

“Ina rokon afuwa, kuma idan aka sake ni b azan kara aikin garkuwa da mutane ba, zan taimaka wajen yakar masu garkuwa, ko kuma in koma yin ko da sana’ar Magi don ciyar da iyalina.” Inji shi.

Legit.ng ta ruwaito duka duka shekarun sa basu wuce 20, amma ya tabbatar da ya kasha akalla mutane 10, kuma ya sha jininsu, sa’annan shi ne shugaban masu garkuwa da mutane dake addaban jama’a a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng