Siyasar Kano: Jam'iyyar adawa ta PDP za ta san matsayin ta a gobe

Siyasar Kano: Jam'iyyar adawa ta PDP za ta san matsayin ta a gobe

Wata babbar kotun jiha a jihar Kano a karkashin jagorancin mai shari'a Justice Nura Sagir zata zartar da wani hukunci a tsakanin jam'iyyar jihar na PDP dake adawa da kuma kuhumar zabe mai zaman kanta ta jihar game da zaben shugabannin kananan hukumomi, gobe.

Mun samu dai cewa jam'iyyar ta PDP a kwanan baya cewa jam'iyyar ta PDP ta shigar da hukumar zaben ta jihar kara kotu inda ta bukaci a tursasa mata ta dage zaben da zata yi ranar 10 ga watan Fabrairu tare kuma da rage kudin fom din takara.

Siyasar Kano: Jam'iyyar adawa ta PDP za ta san matsayin ta a gobe
Siyasar Kano: Jam'iyyar adawa ta PDP za ta san matsayin ta a gobe

KU KARANTA: Ba ruwa na da turanci - Gudaji Kazaure

Legit.ng dai ta samu cewa hukumar zaben jihar ta Kano ta saka Naira dubu 250 ne a kan kowane fom na ciyaman sannan kuma Naira dubu 150 akan fom din ko wane kansila.

A wani labarin kuma, Hukumar nan dake yaki da safarar bil'adama mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya watau National Agency for the Prohibition of Trafficking In Persons (NAPTIP) a turance ta sanar da samun nasarar cafke wani dan shekara 38 mai maganin gargajiya da ya kware wajen sayar da jarirai a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Hukumar dai ta National Agency for the Prohibition of Trafficking In Persons (NAPTIP) ta bayyana cewa mutumin dai sunan sa Mista Chigozie Emmanuel, amma an fi sanin sa da ‘Akuchi’ kuma yana wannan kazamar sana'ar ce a unguwar Nyanya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng