Abin da ya sa nake buga Turanci na babu ruwa na – Hon. Gudaji Kazaure

Abin da ya sa nake buga Turanci na babu ruwa na – Hon. Gudaji Kazaure

- Fitaccen ‘Dan Majalisar Jihar Jigawa yace amfani harshe shi ne sadarwa

- Gudaji Kazaure yace ba Turanci ne a gaba sa ba sai dai kare mazabar sa

- ‘Dan Majalisar yace yana burge mutane da yawa idan ya tashi a Majalisa

Kwanakin baya wani fitaccen ‘Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Jihar Jigawa ya bayyana abin da ya sa bai damu da tsayawa wani gyara harshen Turancin sa ba idan zai yi jawabi a Majalisa sai dai kawai ya fadi abin da za a fahimta.

Abin da ya sa nake buga Turanci na babu ruwa na – Hon. Gudaji Kazaure
Honarabul Muhammad Gudaji Kazaurea Majalisa

Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure mai wakiltar Roni/Gwiwa/’Yan kaushi/Kazaure a Majalisar Tarayya yace sam bai damu da wani Ingilishi idan zai yi jawabi ba, don kuwa ya zo ne domin kare martabar mutanen mazabar sa.

KU KARANTA: Jama'a da dama za su shigi tafiyar mu - Shugaba Buhari

Gudaji Kazaure ya fadawa BBCHausa kwanaki cewa Yankin sa na Jigawa wanda yace kashi 70 na cikin 100 na mutane Yankin sa manoma ne don haka babu dalilin ya zo yana wani dogon turanci illa kawai ya kare ra’ayin su a Majalisar Kasar.

Fitaccen ‘Dan Majalisar yace su kan su abokan aikin na sa a Majalisa yana burge su idan ya tashi zai yi jawabi kuma har a kasar Ingila da ya je yayi Turanci babu wanda yace bai iya ba ko bai gane abin da yake fada bam wanda shi ne muhimmi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng