Matatar mai ta Kaduna ta rufe aiki, saboda karancin danyen mai
- Tun a 1980 aka bude KRPC ta Kaduna
- Tana aiki a kan rabin karfinta saboda tsufa
- An rufe ma'aikatar saboda rashin mai tun 15 ga wannan watan
Ezzakatib Darakta mai kula da ayyuka na matatar mai ta Kaduna, KRPC, Dr. Abdullahi Idris, ya fadi ma ma'aikatansa da 'yan jarida cewa karancin danyen mai ya sanya dole a rufe matatar ya zuwa lokaci na gaba.
Matatar dama na aiki ne da kashi 60 bisa 100 na karfinta saboda tsufa da lalacewar kayan aiki. An dai bude matatar tun 1980, wanda ke nufi shekarun matatar kusan 38. An kuma rufe ta ne makonni biyu da suka wuce a wannan watan na Yanairu.
An mayar da matatar ta Kaduna dai a matsayin ta gwamnati a lokacin mulkin Ummaru 'Yar'aduwa, bayan da Obasanjo ya sayar da ita a 2005 ga Aliko Dangote.
DUBA WANNAN: Kotu ta hana a rataye wani makashi bayan ya manta irin laifin da yayi saboda tsufa
A yanzu dai karancin man fetur zai karu muddin har ba'a tunkudo man na fetur ba, ko danyensa zuwa ga matatar ko depo-depo na tankunanta, saboda masu lodi su diba a tankunan gingimarinsu domin kaiwa gidajen mai.
Matatar dai ita kadai ce a Arewa, cikin matatu 3 da kasar nan ke da su, kuma abun da take tacewa ko jihar Kaduna da sauran yankin baya isa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng