Rikicin siyasar Kano: Zamu kwace kujeran Kwankwaso a 2019 - Ganduje
- Hukumar 'yansandar jihar Kano ta dakatar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga ziyara jihar saboda tsoron barkewan rikici tsakanin magoya bayan sa da na Ganduje
- Gwamnan Abudullahi Ganduje ya ce za su kwace kujeran sanata daga hanun kwankwaso a zaben 2019
Rikicin siyasar Kano na cigaba da habaka yayin da Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso ya dau alwashin shiga jihar Kano a ranar Talata bayan rundunar ‘yansandar jihar Kano ta hana shi shiga.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce, Kwankwaso ba zai dawo kan kujeran sa na sanata a zaben 2019 ba, yayi alkawarin maye gurbin sa da wani dan takara.
Kwanwaso wanda yayi magana ta tsohon kakakin gwamnatin jihar Kano, Dr Rabi’u Sulaiman Bichi, a wani taron manema labaru a Kano, ya ce, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, zai ziyarci jihar Kano a ranar Talata kamar yadda ya shirya.
Ya jadadda haka ne sa’oi 24 bayan kwamishinan ‘yansadar jihar Kano, Rabi’u Yusuf, ya bashi shawara kada ya ziyarci jihar saboda tsoron barkewan rikici tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da na Gandujiyya.
KU KARANTA : Kotu ta umurci wani babba sojan ruwa mai ritaya ya biya wani makiyayi diyyar Naira miliyan N9m ta dalilin tsare masa shanu 42
A ranar juma’a, kwamishinan ‘yansadar jihar Kano ya shawarci, Sanata Kwankwaso ya dakatar da ziyara sa zuwa Kano ko ya fuskanci fushin hukuma idan aka samu matsala a fannin tsaro a jihar.
Ana cikin fargaba a jihar Kano yayin da Gwamna Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka sanya lokacin gudanar da babban taron su a rana daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng