Buhari da Obasanjo sun hadu a wurin taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika
Shugaba Buhari da tsohon shuganban kasa Obasanjo sun hadu a wurin taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika dake gudana a kasar Addis Ababa
Wannan shine karon farko da shugabnnin biyu su ka hadu fuska da fuska tun bayan zungureriyar wasikar da Obasanjo ya aikewa shugaba Buhari yana mai gargadin shi da kul ya sake ya tsaya takara a zaben shekarar 2019 domin ta tabbata cewar ba zai iya mulkin Najeriya ba.
A faifan Bidiyon da muka samu daga shafin Twita na hadimin shugaba Buhari Bashir Ahmed, Shugaba Buhari, ya gaisa da Obasanjo cikin raha kamar yadda zaku iya gani cikin faifan bidiyon. Kazalika shi ma Obasanjo, cikin raha, ya gaisa da Buhari tamkar dai wani abu bai taba shiga tsakaninsu ba.
KU KARANTA: Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani
A nan gida Najeriya, wasikar ta Obasanjo na cigaba da yamutsa hazo a fagen siyasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng