Nigerian news All categories All tags
Siyasar Zamfara: Mutanen da ke shirin gaje kujerar Gwamna Yari

Siyasar Zamfara: Mutanen da ke shirin gaje kujerar Gwamna Yari

- An fara tseren takarar kujerar Gwamna Yari da ke shirin barin mulki

- Daga cikin masu neman kujerar akwai har Mataimakin Gwamna Yari

- Haka kuma akwai Kwamishinoni, da Sanatoci da ‘Yan Majalisar Jihar

Mun kawo maku jerin Mutane 5 da ke shirin gaje kujerar Gwamnan Jihar Zamfara Abdulazeez Yari wanda wa’adin sa zai cika a 2019. Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto akwai wasu mutame 3 yanzu haka a Gwamnatin sa.

Siyasar Zamfara: Mutanen da ke shirin gaje kujerar Gwamna Yari

An fara rububin kujerar Gwamnan Zamfara Yari

1. Muttaka Rini

Alhaji Muttaka Rini wanda shi ne kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Zamfara yana cikin masu neman tsayawa takarar Gwamna a Jihar kuma ana cewa Gwamna Yari ya taba taka masa burki.

KU KARANTA: An nemi PDP ta tsaida Dankwambo takara a 2019

2. Aminu Jaji

Honarabul Aminu Sani Jaji wanda ke wakiltar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Majalisar Tarayya yana cikin masu harin kujerar sai dai Jaji ya fito ne daga Arewacin Jihar wanda da wuya ya samu tikiti.

3. Ibrahim Wakkala

Wakkala Muhammad wanda shi ne Mataimakin Gwamna Yari na iya zama Gwamnan Jihar musamman ganin ya fito daga Yankin da ba su taba mulki ba kuma har su Yerima na bayan sa.

4. Mahmud Shinkafi

Tsohon Gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi yana cikin masu neman Gwamna a 2019 bisa dukkan alamu kuma ya dawo Jam’iyyar APC mai mulki bayan ya bar PDP.

5. Kabiru Marafa

Sanata Jihar na Zamfara Kabiru Marafa zai so ya samu kujerar Gwamnan a 2019, kuma ya fito ne shi me daga Yankin da ba su taba mulkin Jihar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel