Dalilin da ya sa mu ka yafewa Rahama Sadau - Shugaban hukumar tace fina-finan Hausa
- Shugaban hukumar tace fina-finan Hausa Isma'ila Na'abba Afakallah ya yi bayanin dalilan hukumar na yafewa Rahama Sadau
- A kwanakin baya ne hukumar ta sanar da janye dakatarwar da ta yi wa Rahama Sadau tun cikin shekarar da ta gabata
- Sai dai kungiyar taurarin wasan Hausa ta MOPPAN ta ce har yanzu ba ta janye takunkumin da ta kakabawa Sadau din ba
A kwanakin baya ne hukumar tace fina-finan Hausa ta bayyana janye dakatarwar da ta yi wa shahararriyar jarumar wasan kwaikwayon Hausa, Rahama Sadau, tun a shekarar da ta gabata.
A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, shugaban hukumar tace fina-finan masana'antar Kannywood, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya bayyana dalilan da ya saka hukumar sa janye dakatarwar da ta yi wa jarumar.
Afakallah ya ce "Ina son jama'a su sani cewar hukumar tace fina-finai ba wai tana duba halayyar mutum bane wajen yin hukuncinta, muna duba abinda fim din mutum ya kunsa ne."
A cewa Afakallah, akwai yarjejeniya tsakanin masu shirya fina-finan Hausa da masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood cewar duk inda mutum zai shirya fim ko ya fito a cikin wani fim koda kuwa ba'a Najeriya ba ne, zai kasance wakilin jama'ar Hausawa da kuma kare al'adun Bahaushe.
"Mun ja wannan layin amma sai muka samu Rahama Sadau ta ketara shi ta hanyar shirya wani fim a Jos da ya saba da al'adar Bahaushe," a cewar Afakallah.
DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta sha da kyar a hannun wasu matasa
Wannan kuma, a cewar Afakallah, shine dalilin dakatar da jarumar da kuma haramta faifan bidiyon domin tsaftace masana'antar Kannywood da kuma zama darasi ga masu karya dokokin masana'antar shirya fina-finan Hausa.
"Jarumar ta yi nadama kuma har a rubuce ta aiko mana da takardar neman afuwa bayan ta shiga kafafen watsa labarai a Kano ta nemi gafarar Sarki da gwamnan Kano da jama'ar Kano baki daya. Bamu da wani dalili na kin yafe mata," inji Afakallah.
Saidai kungiyar jarumar wasan Hausa da Afakallah ya taba shugabanta, wacce kuma Kabiru Maikaba ke jagoranta, ta ce har yanzu dakatarwar da ta yi wa Sadau din na nan daram.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng