In Buhari ya dage, zamu yaga APC kamar yadda muka yi wa PDP

In Buhari ya dage, zamu yaga APC kamar yadda muka yi wa PDP

- A cikin APC akwai wadanda basu tare da Buhari

- Wasunsu dama daga PDP suka zo don neman takara

- Wasunsu gwamnoni ne da ke da nasu muradin na kashin kansu, ko na oganninsu

In Buhari ya dage, zamu yaga APC kamar yadda muka yi wa PDP
In Buhari ya dage, zamu yaga APC kamar yadda muka yi wa PDP

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya furta cewa, muddin shugaba Buhari ya dage sai yayi takara a cikin jam'iyyar sa ta APC a 2019 to lallai zasu fice daga jam'iyyar su koma wata ko su kafa tasu.

Ya dai yi shagube inda ya furta cewa, muddin jama'armu suka dage cewa mu kare musu nasu muradun to lallai zamu fice daga APC, wadda ke nuni da yana bayan tsohon gwamnansa kuma shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki.

DUBA WANNAN: Anyi kira ga Shugaba Buhari da ya kawo karshen Almajirci

Gwamnan ya nuna bijirewa ga uwar jam'iyya da masu mulki a Abuja tun bayan da aka sanyo ogansa a gaba, bayan juyin mulkin cikin gida da ya kwace majalisa daga hannun mutanen shugaba Buhari da APC.

Kwamacalar ta faro ne bayan da PDP da mara wa Bukola Saraki baya aka yi auren shuwagabannin majalisaaka kada wadanda jam'iyya yi nune da su za'a yi.

Barazanarsa na iya zame wa babban kalubale, domin su ne gwamnoni 7 da suka yi wa PDP tawaye a 2013 inda suka yaga ta biyu, suka kuma kayar da ita a zabe bayan sun gama kai da 'yan adawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng