Nigerian news All categories All tags
An dakatar matuka jirgin sama su biyu bayan sunsha dambe a yayin tukinsu

An dakatar matuka jirgin sama su biyu bayan sunsha dambe a yayin tukinsu

- An dakatar da su shekara biyar a kan fada bayan suna sama

- A kasar Indiya abin ya faru a wani abin al'ajabi

- Sun dambata a sama baayan su ne matukan jirgin

An dakatar matuka jirgin sama su biyu bayan sunsha dambe a yayin tukinsu

An dakatar matuka jirgin sama su biyu bayan sunsha dambe a yayin tukinsu

A kasar Indiya wani hukunci ya hau kan wasu Pilots, watau matuka jirgin sama, bayan da suka dambata a dakin tuka jirgi a sama a watan jiya, bayan suna kan aikinsu a doguwar tafiya a ranar 1 ga watan Yanairu.

Jirgin dai makare yake da fasinjoji, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa hutun karshen shekara, daga birnin Landan zuwa Mumbai, inda kamfaninsu ya kore su daga aiki, hukumomin Indiya kuma suka dakatar da lasisinsu.

DUBA WANNAN: Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajirci

Matuka jirgin mace da namiji sun yi ffada ne inda har shi shugaban tukin jirgin watau Captain ya dalla wa co-pilot watau mataimakiyarsa mari, inda ita kumma ta fice daga dakin tuka jirgin ta barshi da tukin shi kadai, a wani mataki mai hadari sosai.

An dai rike ta sosai kafin ta dawo kan aikinta domin a samu a sauke jirgin na Jet Airlines, wanda mutum daya ba zai iya ba.

Da aka tambayi bahasin me ya faru yayin bincike, sun dai ce rashin fahimtar juna ne ya sa su gaurewa da rikicin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel