An kama wani kirista dan kungiyar Boko Haram a kasar Jamus

An kama wani kirista dan kungiyar Boko Haram a kasar Jamus

Wasu mutane da suka shigar da kara a kasar Jamus dake a nahiyar turai sun sanar da samaun nasarar kama wani dan Najeriya mai suna Amaechi Fred O. mutumin da ake zargi da zama mamba daya daga cikin manyan mayakan Boko Haram da ke tada kayar baya a Najeriya.

Mutumin dai mun samu daga majiyar mu cewa dan shekaru 27 ne kuma ya shiga hannun jami'an tsaron kasar ta Jamus ne a ranar Larabar da ta gabata a yankin garin Bavaria, kuma tuni bincike ya nuna cewa ya na daya daga cikin mayakan kungiyar da suka taba kai hari a wata makaranta da wani kauye dama yin garkuwa da mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

An kama wani kirista dan kungiyar Boko Haram a kasar Jamus
An kama wani kirista dan kungiyar Boko Haram a kasar Jamus

KU KARANTA: An bukaci Buhari ya kawo karshen almajirance

Legit.ng ta samu kuma cewa bisa ga bayanan da aka bada, Amaechi Fred ya zama mamba na kungiyar a shekarar 2013 ya kuma taimakawa kungiyar wajen kai wasu hare-hare hudu da mayakan suka kaddamar a kan jama'a a tsawon shekara guda da ya yi a karkashin kungiyar.

Tuni dai aka shigar da kara don soma gudanar da shari'a kan mutumin.

A wani labarin kuma, A wani labarin kuma, Babbar hukumar nan dake kula da jin dadin mahajjata tare da kula da mahajjatan watau National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) a turance ta fitar da wani sakamakon tantancewa da suka yi wa kamfanonin jigilar mahajjatan shekarar bana.

Sakamakon dai na tantancewar da ya fito ya amince da kamfanoni tis'in sannan kuma ya yi fatali da wasu kamfanonin akalla hamsin da hudu duk dai game da jigilar mahajjatan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng