Wani tsoho mai shekaru 78 yayi wa dan ta wanka da ruwan guba a Najeriya
Wani tsohuwa da ake kyautata zaton ya samu tabuwar hankali mai suna Joseph Adetunji yanzu yanka yana fuskantar tuhuma a gaban wata kotun majistare dake zamanta a garin Legas bisa laifin yi wa dan sa wanka da ruwan guba a fuska.
Shi dai tsohon, Mista Adetunji da ke da shekaru akalla 78 a duniya an gurfanar da shi ne a gaban kotun jiya juma'a tare da wanda ya watsawa ruwan gubara mai suna Mista Abayomi Balogun mai shekaru 60.
KU KARANTA: Maganin karfin maza ya kusa kashe wasu maza
Legit.ng ta samu cewa mai gabatar da kara dai ya shaidawa kotun cewa laifin da ya aikata ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan sannan kuma ya bukaci kotun ta hukun ta shi yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, A wani yunkuri na tabbatar da lafiyar shugabannin kasar Najeriya, kungiyar likitocin Najeriya da kuma likitocin kasashe rainon kasar Ingila sun bukaci a rika yi wa 'yan takara gwaji domin tabbatar da koshin lafiyar su.
A cewar kungiyoyin, wannan matakin idan har aka dauke shi to ba shakka zai taimake su wajen tabbatar da samun shugabannin kasa masu cikakkar lafiya da za su kai kasar ga tudun-ka-tsira.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng