Kungiyar CAN ta zargi shugabanin addinin musulunci da goyon bayan makiyaya
- Kungiyar CAN ta mayar da martani ga kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI)
- Kungiyar CAN din ta zargi shugabanin addinin musulunci da goyon bayan hare-haren da makiyaya ke kaiwa yan Najeriya
- Kungiyar ta CAN ta kuma ce shugabanin na JNI ba su taba fitowa sunyi tir da hare-haren makiyayan ba
A ranar Juma'a ne Kungiyar mabiya addinin Kirista na Najeriya (CAN) ta yi ikirarin cewa shugabanin Kungiyar musulunci na Jama'atu Nasril Islam (JNI) na goyon bayan hare-haren da makiyaya ke kai wa a sassan kasar nan.
Sakatare Janar na Kungiyar CAN, Rabarand Musa Asake ne ya yi wannan zargin a yayin da ya ke mayar da martani akan zargin da shugabanin (JNI) sukayi na cewa shugabanin Kungiyar Kirista na asasa rikici a Najeriya.
DUBA WANNAN: Ministan Tsaro ya bayyana musabbabin kashe-kashen da ke faruwa
A sanarwan da ta bayar kwanakin baya, Kungiyar na Jama'atu Nasril Islam karkashin Jagorancin Sultan Sa'ad Abubakar ta bakin Sakataren Kungiyar, Khalid Aliyu ta zargi shugabanin Kirista da asasa kiyaya da rashin jituwa tsakanin yan Najeriya.
Kungiyar ta CAN ta ce Shugabanin na musulunci goyon bayan makiyayan kamar yadda suka mara wa yan Kungiyar Boko Haram baya a lokacin da suka fara yadda koyarwan su domin suna tunanin yada musulunci suke yi.
CAN ta kara da cewa Kungiyar ta Jama'atu Nasril Islam ba ta fito tayi tir da hare-haren makiyayan ba tun lokacin da suka fara kai hare-haren da ya yi sanadiyar mutuwar yan Najeriya da dama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng