Dubi hotunan yadda Sojin Najeriya sukayi fata-fata da 'yan Boko Haram a Sambisa
Jami'an Hukumar Sojain Najeriya na 'Lafiya Dole' da ke gudanar aikin kakabo ragowar mayakan Boko Haram da ke buya a dajin Sambisa da Arewacin Borno sun sami babbar nasara idan sukayi fatafata da wani sansanin mayakan Boko Haram.
A samamen da Hukumar Sojin suka kai da hadin gwiwar Sojin Sama na Najeriya, sun halaka yan ta'ada guda 7 da jima wasu munanan raunnuka, sun kuma kwace motocin yaki, bindigogi, kayayakin hada bama-bamai, alburusai da sauran su, motoci, kekuna da sauran, Injin janareta, na'aurar rubutu, kakin soja da sauran su.
Wannan nasarar da Jami'an sojan suka samu ya sa Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar IM Yusuf ya ziyarci inda Sojojin sukayi artabu da 'yan ta'adan domin ya kara musu kwarin gwiwa.
KU KARANTA: Ministan Tsaro ya bayyana musabbabin kashe-kashen da ke faruwa
Hukumar na Soji tana kira ga al'umman Jihar ta Borno su taimaka wa Jami'an da bayyanan sirri da ka iya taimakawa rundunar wajen kawar da 'yan ta'addan.
A yayin musayan wutan, Jami'an Soji guda biyu san sami rauni kuma a halin yanzu an garzaya da su asibiti domin karaban magani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng