Almundahanar N11bn: Kotun ƙoli ta umarci Shema ya fuskanci shari'a
A ranar Juma'ar da ta gabata ne, kotun ƙoli ta tabbatar da tuhuma na laifukan cin hanci da rashawa na wawuson kuɗin gwamnati da suka tasar ma naira biliyan 11 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.
Sakamakon hukunci guda ɗaya, Mai shari'a Sidi Bage ya tabbatar da cewa, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa wato EFCC, ta na da cikakkun dalilai da hujjoji na tuhumar tsohon gwamnan, saboda haka duba da tanadi da kotun tayi, ta baiwa hukumar ta EFCC izinin bincike tare da tuhumar duk wanda take zargi da aikata laifukan rashawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, waɗanda ake zargi; Shehu Shema, Sani Hamisu Makana, Lawal Ahmad Safana da kuma Ibrahim Lawal Dankaba, sun ƙalubalanci hukuncin babbar kotun jihar Katsina da kotun ɗaukaka ƙara ta jihar Kaduna a shekarar 2017, wanda suka bayar ta aminci akan zargin.
Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin su ne da yin sama da faɗi da kasafin kuɗi na ƙananan hukumomin jihar domin amfanin kawunan su.
KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya a jihar Binuwai: Gwamna Ortom ya caccaki ministan tsaro na Najeriya
Tsohon gwamnan da sanadin lauyan sa, A.T Kehinde ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ba ta yi masa adalci ba, duba da cewar gurfana a gaban kotu zai zamto barazana ga 'yancinsa na ɗan Adam.
A baya can, Shema da sauran waɗanda ake zargi, sun ƙalubalanci shari'ar su a gaban Mai shari'a Maikata Bako na babbar kotun jihar Katsina, inda suka ce hukumar EFCC ba ta ikon gurfanar da su a ƙarƙashi dokar da gwamnatin jihar ta kafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng