Dan shekara 17 yayiwa mahaifinsa duka har lahira a jihar Bauchi
Wani matashi mai shekaru 17, Nuhu Bulu daga shashin Boloji, karamar hukumar Toro dake jihar Bauchi ya kashe mahaifinsa, Bulus Azi.
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ne suka gurfanar da yaron tare da wasu masu laifin a ranar Alhamis.
A cewar kakakin rundunar, DSP Kamal Datti,yaron ya kashe mahaifin nasa ne ta hanyar buga masa tunkunyar kasa, sanda da kuma karfe.
Yan sandan sun sabar da cewa wasu kannen mai laifin Samaila Bulus da Musa Bulus ne suka kai karar al’amarin ga yan sandan Toro a ranar 17 ga watan Janairun 2018.
Sun rahoto cewa sun bar dan uwan nasu tare da mahaifinsu sannan suka dawo suka tarar da mahaifin nasu da raunuka a kai.
Daga baya aka dauki mahaifin nasu zuwa babban asibitin Toro inda likita ya tabbatar da mutuwar nasa sannan aka kama mai laifin daga baya.
KU KARANTA KUMA: Badakalar N11b: Kotun koli ta yi umurnin tsohon gwamna da wasu 3 su fuskanci shari’a
Da yake Magana da manema labarai bayan an gurfanar da su, Nuhu Bulus ya bayyana gaskiya cewa sun samu sabani ne da mahaifinsa inda daga bisani ya bugi mahaifin nasa a kai da makamai daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa ya aikata laifin ne sakamakon shan kwayoyin maye da yayi.
Kakakin yan sandan yace za a gurfanar da mai laifin a kotu bayan bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng